ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan shi ne taron farko wanda shuwagabannin kasashen 7 suka gudanar tun bayan bullar cutar korona a karshen shekara ta 2019.
Ya zuwa yanzu dai kasashen sun kudurin anniyar taimakawa kasashen marasa karfi da alluran riga kafin cutar korona har billiyon guda.
Labarin ya kara da cewa mafi yawan tattaunawar kasashen an yisu ne a kebe ba tare da ‘yan jarida ba.
Kasashen G7 dai su ne Amurka, Burtaniya, Faransa, Canada, Jamus, Itali da Japan. Banda haka an kira kasashen Indiya, Korea ta Kudu da kuma Autralia zuwa taron.
342/